Dangote zai gina kamfanin taki mafi girma a ƙasar Habasha
A wani mataki na bunkasa tattalin arziƙinta, ƙasar Habasha ta ƙaddamar da fara amfani da babbar tashar samar da iskar gas ta ƙasar, yayin da a hannu guda kuma ta ware dala biliyan goma don fara aikin gina matatar mai da iskar gas
Firaministan ƙasar Abiy Ahmad wanda shi ne ya ƙaddamar da turmin farko na aikin a ranar Alhamis, ya ce suna ci gaba da ƙoƙarin ganin sun maido da ƙasar ta zama gagarabadau a duniya
A yanzu haka ana sa ran za a rika fitar da lita sama da miliyan 100 na gas, yayin da kuma a ɗaya hannun za a samar da megawat dubu guda na hasken lantarki daga wannan tasha.
Bugu da ƙari Abiy ya kuma ƙaddamar da fara aikin wata tashar samar da iskar gas ɗin mai gwaɓin gaske, wanda ake sa ran zai rika samar da lita biliyan guda da miliyan ɗari uku duk shekara
Baya ga wannan katafaren aiki, Firaministan ya kuma ce akwai wani haɗin gwiwa da rukunin kamfaninin Dangote da ƙasar ta yi, inda za ta gina kamfanin taki da aka ƙiyasin kuɗinsa ya kai dala biliyan biyu da rabi
Sai dai Dangote shi ne zai riƙa karbar kashi sittin cikin ɗari na ribar da aka samu, yayin da sauran arba’in kuma ƙasar ta Habasha ce za ta amfana – idan aka kammala aikin kamfanin takin, an ce zai riƙa fitar tan miliyan uku ne duk shekara
Wannan ayyuka suna zuwa ne wata guda, bayan da Habashar ta ƙaddamar tashar samar wuta mai amfani da ruwa mafi girma a duk faɗin Nahiyar Afirka wanda zai riƙa samar megawat dubu biyar duk rana.
Ita dai Habasha tana ta biyu ne a yawan al’umma a nahiyar Afirka inda take da yawan jama’a sama da miliyan 130, bayan Najeriya mai mutane sama da miliyan 230

