Ƴan ƙunar baƙin wake sun kashe mutane goma a Pakistan
Wani harin bam ya kashe aƙalla mutane goma, yayin da wasu talatin kuma suka jikkata a yayin harin mafi muni da aka kai a baya-bayannan a ƙasar Pakistan.
Rundunar ƴansandan ƙasar ta ce sai da suka yi bata-kashi da ƴanbindigan, waɗanda suka sauƙa cikin wata motar alfarma, gabannin daga bisani suka ɗana wannan bam kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Associated Press ta ruwaito.
Rahotanni sun bayyana cewa ƙarar tashin bam ɗin ya firgita al’umma da dama na kusa da ma nesan gurin da abin ya faru, abinda ya sa ba a samu jinkirin zuwan ma’aikatan ceto ba.
Wani faifayin bidiyo ya nuno yadda maharan suka dirka daga wata mota a gaban tungar jami’an soji inda sauƙarsu ke da wuya aka fara bata-kashi – kuma tuni aka hallaka maharan baki ɗayansu.
Motoci da tagunan gine da wasu ƙadarori ne aka yi hasararsu sakamakon wannan hari, Kodayake har kawo yanzu mahukunta ba su bada rahoton ko an samu hasarar rai daga ɓangaren jami’an tsaro ba.
Sai dai jama’a na ci gaba da zaman zulumi a birnin na Quetta, bayan harin na ranar Talata.

