Latest NewsNational News

Mahmud Yakubu ya sauka daga kujerar shugaban hukumar INEC

Shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa INEC, Farfesa Mahmud Yakubu ya yi murabus daga kan kujerarsa, inda ya miƙata ga babbar Kwamishina a hukumar wato May Agbamuche

Farfesa Mahmud Yakubu ya hau kukerar ne tun a shekarar 2025, inda ya shafe shekara goma yana jan ragamarta, abinda ya bashi damar gudanar da wa’adi biyun da doka ta sahale masa

Farfesa Yakubu ya bayyana saukar tasa ne a ranar Talata a lokacin ganawarsa da kwamishinonin hukumar a ofishin zaɓen da ke birnin tarayya Abuja.

A yanzu haka Agbamuche wacce ta fi kowa ɗaɗewa a matsayin babbar kwamishina a hukumar zaɓen ƙasar, za ta riƙe muƙamin ne har zuwa lokacin da za a naɗa mata shugaba

A watan Oktoba 2015 ne tsohon Shugaban Najeriya Marigayi, Muhammadu Buhari ya naɗa Farfesa Yakubu a matsayin shugaban hukumar INEC, wanda ya maye gurbin Farfesa Attahiru Jega.

Ba a yi ƙasa a gwiwa ba dai, a 2020 Muhammadu Buhari ya sake naɗa shi a karo na biyu don jagorantar hukumar a wa’adi na biyu.

Farfesa Yakubu ya jagoranci hukumar na tsawon shekara 10, tare da gudanar da manyan zabukan kasar biyu na 2019 da kuma 2023.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *