Gwamnatin Taraiya ta kashe ƴan ta’adda 13,500 ta kuma kama 17,000 a shekaru biyu – Minista
Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa hukumomin tsaro sun kashe sama da ƴan ta’adda 13,500 tare da kama fiye da 17,000 da ake zargi da hannu a ta’addanci tun bayan da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya hau mulki a watan Mayu 2023.
Ministan yada labarai , Mohammed Idris, ne ya bayyana hakan a taron manema labarai da aka gudanar a Abuja ranar Laraba.
A cewarsa, an kuma kubutar da mutane 9,800 da aka sace, ciki har da mata da yara, yayin da ‘yan ta’adda 124,000 da iyalansu suka mika wuya tare da mika makamai 11,000 ga gwamnati.
Idris ya ce an kashe manyan shugabannin ta’addanci kamar Ali Kachala, Boderi da Halilu Sububu, yayin da hare-haren tashin hankali a Kudu maso Gabas suka ragu da kashi 80 cikin 100.
Ya kara da cewa daruruwan mutane na fuskantar shari’a kan laifukan ta’addanci, ciki har da shugabannin Ansaru da wasu da ake zargi da hannu a harin Cocin Katolika na Owo da kisan Yelwata a Jihar Benue.
Ministan ya ce mutane 125 an riga an yankewa hukunci, inda ya jaddada cewa gwamnati ba za ta huta ba har sai an gama da sauran mayakan ta’addanci a kasar.

