Labarai

Hatsarin mota ɗauke da Hakimi ya sa an gano manya-manyan ƙullin tabar wiwi 387 a Bauchi

Rundunar ƴansandan jihar Bauchi ta sanar da cafke ganye wiwi kimanin 387 a yayin wani hatsarin mota a Bauchi

Hatsarin ya auku ne a ranar 4 ga watan Oktoba 2025 a ƙauyen Wom dake ƙaramar hukumar Toro wuraren 11:30am

Kakakin rundunar CSP Ahmed Mohammed Wakil ya shaida a cikin wata sanarwa da ya fitar cewa, wannan mummunan hatsarin ya rutsa ne da wasu motoci guda biyu ƙirar Toyota Corolla ciki har da Hakimin ƙauyen Nabordo Suleiman Bala Suleiman tare da direbansa Ali Muhammad mai shekara 45, yayin da suke hanyarsu ta komawa gida Nabordo daga birnin Bauchi

CSP Ahmed Wakil ya ce Hakimin sun yi taho-mu-gama ne da ɗaya motar mai lamba GWA-155GW, yayin da ya yi yunƙurin wuce wata, inda ba tare da hankalta ba ne aka gwabza

Ganau sun shaida cewa mutumin ya fito birnin Jos ne na Jihar Pilato lokacin da ya yi wannan yunƙuri.

Hatsarin ya yi sanadiyar raunuka da dama ciki har da karaya da Hakimin ya samu a ƙafarsa ta hagu – kuma tuni aka garzaya da su asibitin koyarwa na jami’ar Abubakar Tafawa Balewa dake Bauchi don ci gaba da duba lafiyarsu

Daga cikin abubuwan da aka samu a motar da ta fito Jos ɗin akwai, ganyen wiwi ƙulli 387, da jaka ɗauke da muhimman abubuwa na mai ita, da ƙananan leda su ma ɗauke da abubuwa masu muhimmanci gami da wayar hannu ƙirar Tecno ba tare da layi a ciki ba

Sauran abubuwan a cewar Wakil, sun haɗa da lasisin tuƙinda kuma takardun mota mai ɗauke da rajistar Abuja GWA-155GW, ba tare da makullin motar ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *