Labarai

Gidauniyar Wunti Al-khair ta Tallafa da Fitilun Titi na Solar a Unguwar Wunti

Daga Ismail Bauchi

Gidauniyar Wunti Al-khair ta samar da fitilun titin da ke amfani da hasken rana (solar) a wurare daban-daban na unguwar Wunti, a wani yunƙuri na ƙara tsaro da inganta rayuwar al’ummar yankin.

Yayin bikin miƙa fitilun a hukumance a Wunti, wakilin gidauniyar, Barista Umar Magaji, ya ce wannan aiki wani ɓangare ne na nauyin da gidauniyar ta ɗora wa kanta na kula da al’umma.

Barista Magaji ya bayyana cewa, gidauniyar ta shafe shekaru tana samar ayyukan da ke da tasiri kai tsaye ga rayuwar jama’a, inda ya ƙara da cewa aikin samar da fitilun zai taimaka rage aikata laifuka, ya bunƙasa harkokin kasuwanci da tsaro a lokacin dare, tare da sauƙaƙa rayuwar jama’a.

Ya kuma tabbatar wa al’ummar Wunti cewa gidauniyar za ta ci gaba da jajircewa wajen samar da ayyukan jin ƙai a sassa daban-daban na Jihar Bauchi, domin tallafa wa ƙoƙarin gwamnati na cigaban al’umma.

Tun da farko, mai kula da aikin, Injiniya Maxwell Patrick, ya bayyana cewa wurare guda shida a cikin unguwar aka samar musu da fitilun titin solar masu ƙarfin 400-watt kowanne.

Ya jaddada cewa wannan fasaha ce da ke da matuƙar amfani wajen kare muhalli tare da rage kuɗin amfani da wutan lantarki.

A nasa jawabin, Mai Unguwar Wunti, Alhaji Buhari Baban’ya, ya yaba wa gidauniyar Wunti Al-khair bisa wannan gagarumin aiki, yana mai cewa hakan zai taimaka matuƙa wajen rage rashin tsaro, sauƙaƙa zirga-zirga a lokacin dare, tare da ƙara bunƙasa harkokin zamantakewa da na kasuwanci a yankin.

Alhaji Baban’ya ya kuma yi kira ga sauran masu hannu da shuni da ƙungiyoyi masu zaman kansu da su yi koyi da gidauniyar, ta hanyar tallafa wa ayyukan al’umma da za su inganta rayuwar jama’a. Ya tabbatar da cewa al’ummar Wunti za su kula da kayan da aka samar domin tabbatar da dorewarsa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *